Kasar Moroko Ta Lashe Kofin Kasashen Larabawa

Kungiyar kwallon kafa ta Moroko ta lashe kofin kasashen larabawa bayan da ta buga da kasar Jordan, a kasar Qatar a ranar Alhamis. A can

Kungiyar kwallon kafa ta Moroko ta lashe kofin kasashen larabawa bayan da ta buga da kasar Jordan, a kasar Qatar a ranar Alhamis.

A can birnin Rabat babban birnin kasar ta Moroko masu sha’awar kwallon kafa sun fito kan tituna domin nuna murna akan nasarar da kasar tasu ta samu na lashe kofin kasashen larabawan.

A cikin watan Ogusta ne dai kungiyar wasan kwallon kafa ta  lashe wasan cin  kofin Afirka, sai kuma kungiyar ‘yan kasa da shekaru 20, ta kasar ta ci kofin duniya a watan Oktoba, yanzu kuma ta zama zakarar kasashen larabawa.

Kasahen larabawa 16 ne dai su ka buga da juna a birnin Doha na kasar Qatar domin lashe kofin kasashen larabawan. Daga cikin kasashen da su ka yi gasar da akwai 6 da su ka fito  daga nahiyar Afirka.

Moroko ta zura kwallaye 3 a ragar Jordan, yayin da ita kuma aka zura ma ta kwallaye 2.”Yan kasar ta Moroko suna fatan ganin kasar tasu ta lashe kofin nahiyar Afirka mai zuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted