Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya ce; Moscow ta bukaci ganin shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta duniya Refael Grossy ya zama dan baruwanmu akan batun makamashin Nukiliya na Iran, ya yi amfani da kwarewa a cikin aikinsa.
Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya nakalto Lavrov da ya gabatar da taron manema labaru a jiya Juma’a yana cewa; Abinda Moscow take son gani daga grossy shi ne aiki da ka’idojin aiki da kaucewa goyon bayan wani bangare.
Bayan harin da aka kai wa cibiyoyin Nukiliyar Iran, wanda ba ya kan doka, alaka a tsakanin Tehran da hukumar ta ( IAEA) ya fuskanci koma baya. Bugu da kari majalisar shawarar musuluncin Iran ta yi dokar da ta hana aiki da ( IAEA) har sai daya bangaren yarjejeniyar ya yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansa.
A halin yanzu Amurka da kasashen turai uku,Jamus, faransa, da Ingila suna ci gaba da shigar da siyasa a cikin batun makamashin nukiyar ta Iran.
Jamhuriyar musulunci ta Iran dai ta sha nanata cewa, za ta mu’amala ne da hukumar makamashin Nukiliyar a karkashin dokar majalisar shawarar musuluncin ta Iran.
Shi kuwa kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’ila Bakai’ ya bayyana cewa; har yanzu Iran tana nan a cikin yarjejeniyar hana yaduwar makamashin Nukiliya.