Amurka Ka Kai Hare-Haren Daukar Fansa Kan ISIS A Kasar Siriya

Gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan cewa ta kai hare-hare ta sama da kasa a wasu yankuna a kasar Siriya don halaka mayakan ISIS wadanda

Gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan cewa ta kai hare-hare ta sama da kasa a wasu yankuna a kasar Siriya don halaka mayakan ISIS wadanda take zargi da kashe sojojin Amurka biyu a yankin Palmyra na tsakiyar kasar ta Siriya.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yaki na kasar Amurka Pete Hegseth an kai hare-haren ta sama da ta kasa, da nufin kawo karshen mayakan ISIS nda suke rage a kasar ta Syiria.

A cewar wasu daga cikin jami’an gwamnatin kasar Amurka dai, itace ta samar da kungiyar ISIS don bawa kanta damar mamayar kasashen Iraki da siriya a shekara ta 2014.

Kuma a halin yanzu shugaban kasar Siriya da suka nada bayan faduwar gwamnatin Bashar al-asad tsohon dan kungiyar ta ISIS ne.

Tun lokacin faduwar gwamnatin Bashar Al-Asad shekara guda da ta gabata, kasar Siriya ta na fama da tashe-tashen hankula da kuma rasgin zaman lafiya a cikin kasar. Akwai kuma alamun suna son rarraba kasar ta siriya ta yadda babu wata kasa da zata yaki HKI a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted