Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar iran Masu’d fezeshkiyan ya jaddada cewa ba zamu taba amincewa da raunanawa ko rarraba kawukan alummar iran ba, yayi gargadin cewa kasashe masu karfi na duniya suna kokari wajen raunana hadin kai da yancin kasar iran ,don haka yayi kira ga alummar iran da su kara hada kansu domin tunkarar kalubalen da suke fuskanta a cikin gida.
Wadannan bayannan na fezeshkiyan ya nuna irin matsayar iran ne na tsawon lokaci game da bukatar da kasashen yamma suka gabatar kan shirin nukiliya, da kuma karfin makamai masu linzami, da rawar da take takawa a yankin don raunata kasar iran din maimaikon warware sabanin dake tsakani.
Haka zalika ya yi gargadi game da abin da wasu suka yi imani cewa kyautata dangantaka sa kasashen turai kawai ne zai iya warware matsalar iran, yana mai ishara game da tattaunawar nukiliya da aka yi a baya, yace ko da iran ta cimma matsaya da shuwagabannin kasahen turai to Amurka zata hana aiwatar da shi.