Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Iran sun jaddada azamarsu ta ganin bunkasa alakarsu a fagagen kasuwanci, zuba hannun jari, makamashi bayan da su ka yi wata tattaunawa a birnin Abuja.
An yi tattaunawar ne a jiya 17 Disamba a ginin ma’aikatar harkokin waje dake Abuja,a tsakanin Dunoma Ahmed wanda shi ne babban satakaren ma’aikatar, da kuma jakadan jamhuriyar musulunci ta Iran a Nigeria, Gholareza Madhavi Raja.
A wata sanarwar da kakakin ma’aikatar harkokin wajen ta Najeriya Kimiebi Ebienfa ya fitar, a yau Alhamis ya ce; Wannan tattaunawar ita ce ta farko a gwamnatance da aka yi, tun bayan da jakadan ya kaddamar da takardunsa na kama aiki ga shugaba Bola Ahmad Tinubu.
A nashi gefen, Raja ya bayyana Nigeria a matsayin abokiyar aiki mai humimmanci a siyasar kasar ta waje, kuma wata kofa ta shiga cikin yammaci Afirka da kuma fadada alakarta da nahiyar Afirka.
Jakadan na Iran a Nigeria, ya yi Ishara da yadda alakar kasashen biyu ta wuce rabin karni, sannan ya nuna rashin jin dadin rashin jakadan Nigeria a Tehran a wannan lokacin.
Sai dai kuma ya nuna farin cikinsa akan yadda a halin yanzu Nigeria din take kokarin ayyana sabon jakada zuwa Iran,tare da cewa hakan zai bunkasa alakar tattalin arziki ta fuskar diplomasiyya.