Kasashen Iran da Rasha sun cimma yarjejeniyoyi da dama a tsakaninsu na karfafa dangantaka.
An bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na hadin guiwa tsakanin Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na Rasha, Sergey Lavrov, .
Manyan batutuwan da aka tattauna sun hada da dangantakar kasashen biyu, hadin gwiwar tattalin arziki, takunkumin kasashen yamma, batun nukiliya na Iran, yakin Ukraine, tashin hankali tsakanin Washington da Caracas, da kuma halin da ake ciki a Kudancin Caucasus.
A yayin taron manema labarai, Ministan Harkokin Wajen Iran ya yi magana kan dangantakar tattalin arziki tsakanin Tehran da Moscow, da kuma takunkumin da aka sanya wa Iran da Rasha.
Domin magance bukatun tattalin arzikin kasashen biyu da kuma dakile takunkumin, Mr. Araghchi ya nuna cewa ana ci gaba da musayar ra’ayoyi, ta hanyar hadin gwiwar tattalin arziki, musamman a fannin sufuri, da makamashi.
Ya kuma sanar da cewa Kwamitin Tattalin Arziki na Hadin Gwiwa tsakanin Iran da Rasha, wanda ya kunshi yarjeniyoyi 17 na musamman, zai gana a watan Fabrairun 2025.
“Kasashenmu biyu, membobin cibiyoyi kamar BRICS, Kungiyar Hadin Gwiwa ta Shanghai, da Kungiyar Tattalin Arziki ta Eurasia, suna ci gaba da hulɗar haɗin gwiwa,” in ji shi, kafin ya jaddada cewa Tehran da Moscow suna da haɗin gwiwa don magance takunkumin Amurka ba bisa ƙa’ida ba da kuma adawa da matakan tilastawa da takunkumin gefe ɗaya.