Shugaban Amurka Donald Trump ya faɗaɗa dokar hana tafiye-tafiye don dakatar da shiga kasar ga karin wasu kasashe biyar na Afirka.
Wannan sabon mataki ya shafi masu fasfo daga Burkina Faso, Mali, Nijar, Sudan ta Kudu, da kuma Saliyo.
Sabon matakan, zai fara aiki a ranar 1 ga Janairu, 2026.
Ga Burkina Faso, Mali, da Nijar, Trump ya ambaci ayyukan ƙungiyoyin ta’addanci a ƙasashen Sahel, yayin da ya kuma ware Burkina Faso saboda ta ƙi karɓar mutanen da aka koro daga Amurka.
Dokar ta kuma sanya takunkumin tafiye-tafiye na dan lokaci ga wasu kasahen Afrika 15, ciki har da Najeriya.
Shugaban Amurka ya ce Najeriya na fuskantar “wahaloli masu yawa na tantancewa saboda “ƙungiyoyin ta’addanci masu tsattsauran ra’ayi na Musulunci kamar Boko Haram da Islamic State dake cin karensu babu babbaka a wasu sassan ƙasar”
A watan da ya gabata, Washington ta zargi masu fafutukar Islama da kai hari ga Kiristoci a Najeriya har ta yi barazanar ɗaukar matakin soja.
Abuja ta yi watsi da ikirarin, tana mai cewa hare-hare suna shafar mutane na kowane addini.