Majalisar Dinklin Duniya ta yi gargadi game da yawan ‘yan jaridan da aka kashe a zirin Gaza, yayin da kuma aka kama sama da 200.
Tsakanin watan Oktoba 2023 zuwa tsakiyar watan Disamba 2025, ‘yan jarida 289 ne suka rasa rayukansu a hare-haren Isra’ila a Gaza, in ji Babban Kwamishinan Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya (OHCHR).
A cewar Ofishin a Yankunan Falasdinawa da aka Mamaye, akwai shaida mai karfi cewa an kai wa ‘yan jaridar Falasdinawa hari da gangan saboda aikinsu.
“Wadannan duk sun toshe wata hanya ta bayyanawa duniya gaskiyar halin da ake ciki a yankin.