Hukumar Agaji ta sanar da cewa sanadiyyar saukar ruwan sama mai yawa a yankin Gaza, Falasdinawa 17 sun rasa ransu, kuma kaso 90% na wuraren da aka warewa ‘yan hijira sun jike a cikin ruwa.
Daga cikin wadanda su ka rasa rayukan nasu saboda sanyi da akwai kananan yara 4, sauran kuwa sun rasa rayukansu sanadiyyar ruftawar gine-ginen da suke a cikinsu.
Mai magana da yawun masu ayyukan agajin Mahmud Basal ya fada wa kamfanin dillancin labarun “Safa” cewa; Da akwai gine-gine fiye da 17 da su ka rushe, tun da aka fara ruwan sama,kuma da akwai wasu gine-ginen 90 da wani bangare nasu ya rushe da hakan yake a matsayin hatsari ga rayuwar dubban mutane.
Basal ya kuma yi ishara da cewa; kusan kaso 90% na cibiyoyin da ‘yan hijira suke ciki, sun nutse a cikin ruwa, kuma ilahirin hemomin da suke a Gaza din sun yi illa.
A halin yanzu dai da akwai dubban ‘yan hijira da su ka rasa matsuguni,kuma tufafinsu da katifunsu na kwanciya duk sun lalace, da hakan yake kara zurfin wahalar da suke ciki.
Haka nan kuma ya yi ishara da yadda hukumar agajin ta sami kiraye-kiraye daga mutane har sau 5000 suna neman taimako. Basal ya kuma yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su kawo dauki na hemomi, da kuma fara sake gina gidajen da yaki ya rusa.
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai MDD ta sanar da cewa da akwai mutane miliyan 1.3 da suke da bukatuwa da taimako,musamman a lokacin da sanyi yake karuwa.
A cikin makwanni kadan da su ka gabata an sami saukar ruwan sama da yawa a yankin na Gaza,lamarin da ya kara wahalhalun Falasdinawan Gaza.