Iran : Duk da wahalhalun da ake ciki, akwai nasarori masu yawa_Jagora

Jagoran juyin juya halin Musulinci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana cewa duk da wahalhalun dake akai a kasar, akwai nasarorin masu yawa

Jagoran juyin juya halin Musulinci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana cewa duk da wahalhalun dake akai a kasar, akwai nasarorin masu yawa da ake samu.

Jagoran ya bayyana hakan ne a taron tunawa da shahidai 5,580 na Lardin Alborz, inda yake cewa: “Duk da wahalhalun da ake fuskanta a yanzu, kasarmu tana cimma kyawawan manufofinta.”

A wannan taron, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya jaddada cewa a yanayin da ake ciki yana da muhimmanci a koyarwa matasa dabi’u na riko da akidar kare tsaron kasa.

Ya kuma ce duk da amfani da wasu hanyoyi na zamani don sanya wasu ra’ayoyi da abubuwa da dama a zukatansu, matasan na kiyaye addininsu.”  

Jagoran juyin juya halin ya bayyana cewa himma da nauyin da ke kan al’umma suna daga cikin kyawawan halaye, sannan ya jaddada cewa bai kamata a bar wadannan kyawawan halaye su gushe a zukatan matasa ba.

Ayatollah Khamenei ya tabbatar da cewa: “Duk da wahalhalun da muke fuskanta, dole ne mu karfafa kyawawan halaye don kare juyin juya halin Musulunci da kuma Musuluncin.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted