Ofishin daukaka kara na Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ya yi watsi da hujjojin Isra’ila da ke kalubalantar ingancin binciken da ta gudanar kan laifukan da aka aikata a Gaza bayan yakin Isra’ila a yankin Gaza da aka kewaye.
Wannan shawara ta zo ne, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan laifukan yaki a Falasdinu, wanda ya kai ga bayar da sammacin kama Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon Ministan Tsaronsa, Yoav Gallant, saboda “laifukan cin zarafin bil’adama da laifukan yaki” da aka aikata a lokacin yakin kisan kare dangi a Gaza.
Isra’ila ta yi kokarin soke sammacin, musamman ta hanyar aza tambaya akan mai Gabatar da Kara na ICC, Karim Khan, da kuma kalubalantar ikon Kotun.
Haka zalika Kotun ta ICC, wacce ke da kasashe mambobi 125, ta dade tana fuskantar suka daga jami’an Amurka wacce kawa ce ga Isra’ila, inda ta kakaba takunkumi kan manyan jami’an Kotu.
A watan Yuli, kafofin watsa labarai sun ba da rahoton cewa an yi wa babban mai gabatar da kara na Kotu, Karim Khan, gargadi idan ba a janye sammacin ba.
Tun daga watan Oktoban 2023, sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa sama da 70,400, galibi mata da yara, tare da raunata wasu 171,000 a Zirin Gaza tare da mayar da yankin kufai.