Iran da Belarus Sun cimma Yarjejeniyoyi Don Kawar da Takunkuman kasashen Yamma

Iran da Belarus sun sanya hannu kan mahimman yarjejeniyoyi guda uku da nufin karfafa hadin gwiwa tsakaninsu da kuma karya tasirin takunkuman kasashen Yamma akan

Iran da Belarus sun sanya hannu kan mahimman yarjejeniyoyi guda uku da nufin karfafa hadin gwiwa tsakaninsu da kuma karya tasirin takunkuman kasashen Yamma akan kasashen nasu.

An cimma wannan ne a yayin ziyarar Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi a birnin Minsk yayin ganawa da takwaransa na Belarus, Maxim Ryzhenkov.

Jami’an biyu sun sake nanata alkawarin kasashensu na inganta hadin gwiwarsu musamman a kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da Majalisar Dinkin Duniya da hukumominta, da kungiyar BRICS, da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), da kuma kungiyar tattalin arziki ta Eurasia (EAEU), da kungiyar ‘yan ba ruwan mu (NAM).

A wani taron manema labarai na hadin gwiwa bayan taron, Mr. Araghchi ya bayyana tattaunawarsa da Shugaban Belarus Alexander Lukashenko da Ministan Harkokin Waje Ryzhenkov a matsayin “mai kyau da mahimmanci.”

“Dangantaka tsakanin Iran da Belarus tana kan hanya madaidaiciya.” “Tun bayan samun ‘yancin kai na Belarus.

Dangantakarmu ta kasance mai kyau, kuma bisa ga muradun juna da girmamawa, kuma za mu ci gaba akan wannan hanya,” in ji ministan harkokin wajen Iran.

A nasa bangaren, Maxim Ryzhenkov ya tabbatar da cewa kawancen da ke tsakanin Tehran da Minsk yana taimakawa wajen inganta muradun kasashen biyu “a manyan fannoni na duniya.

“Ƙasashen Iran da Belarus dukkansu suna fuskantar takunkumin zalinci na kasashen yamma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted