An Yi  Gagarumin Gangamin Nuna Goyon Bayan Shugaba Maduro A Venezuela

A yau litinin an gudanar da jerin gwano da gangami a cikin birnin Caracas da sauran gagaruwan kasar Venezuela domin nuna goyon bayan al’ummar kasar

A yau litinin an gudanar da jerin gwano da gangami a cikin birnin Caracas da sauran gagaruwan kasar Venezuela domin nuna goyon bayan al’ummar kasar ga shugaba Nicholay Maduro da yake fuskantar barazana daga Amurka.

Masu zanga-zangar dai sun yi Allawadai da yadda Amurka ta keta hurumin kasar ta hanyar kwace jirgin ruwa na dakon man fetur a gabar ruwa.

Gwamnatin kasar ta Venezuela dai ta bayyana kwace ma ta jirgin ruwan da Amurkan ta yi a matsayin fashi da makamai a doron ruwa, wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Masu zanga-zangar sun kuma bayyana cikakken goyon bayansu ga yadda shugaban kasar Nicholay Maduro yake  nuna kwazon kare kasar.

A jawabin da ya yi wa al’ummar kasar shugaba Nicholay Maduro ya yi kira da su kasance masu kare kasa, tare da yin Ishara da yadda ake samun sauyi a siyasar duniya da wasu kasashe su ka kawo karfi.

Amurka dai ta kakaba wa man fetur din kasar Venezuela takunkumi tun a 2019, da hakan ya sa kasar  take sayar da man nata da sauki a kasuwannin duniya,musamman ma dai ga kasar China.

 A cikin watannin bayan nan dai kasar Amurka tana kai wa kananan jiragen ruwa da suke fitowa daga Venezuela hare-hare.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted