Wani Dan Majalisar Amurka Ya Bukaci A Janye Dukkan Sojojin Amurka A Siriya

Rahotanni sun bayyana cewa dan majalisar Amurka Ran paul ya sake kira da a kwashe dukkan sojojin Amurka dake kasar siriya, bayan harin da aka

Rahotanni sun bayyana cewa dan majalisar Amurka Ran paul ya sake kira da a kwashe dukkan sojojin Amurka dake kasar siriya, bayan harin da aka kai wa dakarun sojin Amurka a kusa da garin Palmyra a kasar ta larabawa,

Paul ya sake nanata kira ne a jiya lahadi  kwana daya bayan da aka tabbatar da kashe sojojin Amurka guda biyu tare da jikkata wasu guda 3 a garin Hums dake tsakiyar Siriya, kuma ana  zargin wasu mambobin kungiyar Daesh ne suka kai harin.

Yace dole ne a ladabtar da wadanda suka kashe sojojin, amma ya kamata mu sake tunani na yi yuwar ci gaba da zaman sojojin  a siriya ko kuma A’a, wani dan majalisar yace kasancewar sojojin Amurka a kasar siriya ya mayar da wajen a matsayin cibiyar kungiyoyin yan ta’adda a duniya.

Ci gaba da kasancewar sojojin Amurka a kasar siriya ya ci gaba da jawo cece -ku ce ganin cewa tana aiki ne ba tare da amincewar gwamnatin kasar siriya ko kuma amincewar majalisa ba, a watan Aprilu Amurka ta sanar a  hukumance za ta rage yawan sojojinta a Siriya daga 2000 zuwa 1000.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted