Shugaban Ƙasar najeriya Bola Tinubu, ya buKaci shugabannin Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), da su yi tsayin daka wajen hana canza gwamnati ba bisa ka’ida ba, wanda ya yi gargadin cewa barazanar da ke kara bayyana a yankin na bukatar hadin kai da yin aiki tare.
Tinubu, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga shugabannin kungiyar a taron Majalisar Shugabannin kasashen ECOWAS karo na 68 inda ya ce ya zama dole a dauki mataki kan iyakokin kasashen Yammacin Afrika domin magance barazanar tsaro.
Haka zalika ya jaddada cewa babu wata kasa komai girma ko karfinta, da za ta iya tabbatar da zaman lafiya ita kadai, yana mai cewa matsalar tsaro da samar da walwala alhaki ne da yake kan kowa kuma hakan na bukatar hadin kai.
A cewarsa, barazanar da ke fuskantar Yammacin Afrika daga waje sun hada da ta’addanci da masu tsatsauran ra’ayin addini da kuma canza gwamnati ba bisa ka’ida ba da ma sabanin tsakanin kasashe da rashin tsaro a bangaren yanar gizo da ma tasirin sauyin yanayi da karancin abinci da kuma hijira ba bisa ka’ida ba.