Albanese ya goyi bayan tsauraran dokokin mallakar bindiga bayan harin Sydney

Firaministan Ostiraliya Anthony Albanese ya ce, yana goyon bayan tsauraran dokokin mallakar bindiga bayan mummunan harin da aka kai a bakin tekun Bondi na Sydney,

Firaministan Ostiraliya Anthony Albanese ya ce, yana goyon bayan tsauraran dokokin mallakar bindiga bayan mummunan harin da aka kai a bakin tekun Bondi na Sydney, inda ake bikin ranar Yahudawa ta Hanukkah.

“Gwamnati a shirye take ta dauki dukkan matakan da suka dace, wannan ya hada da bukatar karin dokokin mallakar bindiga,” in ji Albanese.

 ‘Yan sanda a kasar dai sun tabbatar da cewa daya daga cikin maharan ya mallaki bindigogi har guda shida bisa doka.

Kawo yanzu dai ‘yan sanda a kasar na ci gaba da bincike bayan harin da aka danganta da na kin jinin Yahudawa wanda ya kashe mutane 16 a jiya Lahadi, a bakin tekun Bondi da ke Sydney yayin bikin Hanukkah.

A cewar kafofin watsa labarai na cikin gida, jami’an leken asiri na ksaar sun riga sun yiwa daya daga cikin maharan biyu, wadanda uba da da ne, alama saboda zargin alaka da kungiyar IS.

Kasashen duniya da dama sun yi tir da Allawadai da harin.

Iran ta yi Allah wadai da harin tana mai danganta shi da “mummunan abu” da aka kai kan wani taron Yahudawa a Sydney.

‘’Muna Allah wadai da harin da aka kai wa fararen hula a Sydney,” in ji mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmaeil Baghaei a cikin wani sako a shafinsa na X.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted