Iran Ta Bukaci Mutanen Yemen Su Daina Kashe Juna

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya gargadi mutanen kasar Yemen daga kungiyoyi daban daban da su yi kokarin sasantawa a tsakaninsu, saboda

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya gargadi mutanen kasar Yemen daga kungiyoyi daban daban da su yi kokarin sasantawa a tsakaninsu, saboda ci gaba ta yakar juna yana taimakawa HKI ne kawau.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baghaei ya na fadar haka a yau Lahadi a cikin wani  bayanin da ya watsa a shafinda na X.

Ya kara da cewa a cikin yan makonnin da suka gabata yan bindiga wadanda suke samun goyon bayan saudia sun fara yaki da sojojin Gwamnatin Yemen a kudancin kasar mai arzikin man fetur da nufin tada hankali a kasar.

Wasu kafafen yada labarai suna maganar cewa kudancin kasar Yemen zata shelanta bellewarta daga arewacin kasar nan ba da dadewa ba.

Baghaei ya bayyana cewa dukkan wadan nan al-amura suna faruwa ne a cikin shirin HKI na sake tsara kasashen yammacin Asiya.  Kuma shi yasa bata barin wata kasa daga kasashen yankin ta ci gaba da zaman lafiya ba.

 Daga karshen ya bukaci kungiyoyi daban-daban a kasar ta Yemen su yi kokarin sasantawa a tsakaninsu kada su ci gaba da aiki wa yahudawa ta hanyar rarraba kansu da kuma zubar da jinanensu don amfanin yahudawa.

Yayi kira ga gwamnatin kasar Yemen ta yi kokarin sasantawa da sauran Kabilun kasar don dawo da zaman lafiya a kasar. Duk wanda bai son zaman lafiya shi ne wanda yake khidima wa makiyan kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted