Ghana Ta Kori Wasu Yahudawa Guda 3 Don Mayar Da Martani

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin kasar Ghana ta kori wasu yahudawa guda 3 daga kasar domin mayar da martani kan matakin da isra’ila ta dauka

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin kasar Ghana ta kori wasu yahudawa guda 3 daga kasar domin mayar da martani kan matakin da isra’ila ta dauka na korar yan kasarta ta filin hawa da saukar jiragen sama na Ben Gurion.

Wannan mataki ya aike da wani sakon diplomasiya ne dake nuna cewa kasar Ghana a shirye take ta dauki matakin mayar da martani don kare martabar kasarta da hakkin yan kasarta kan duka wani matakin cin zarafi da isra’ila za ta dauka .

Ma’aikatar harkokin wajen Kasar Ghana tace  tana kimanta duk wata dangantaka dake takaninta da kasashe don haka tana sa rana za’a girmama yan kasarta a duk mua’malar da za’a yi da su kamar yadda sauran kasashe ke sa ran ita ma za ta yi mua’amala cikin girmamawa da mutunta yan kasarta.

Tuni dai kasar ghana ta gayyaci mai kula da ofishin  jakadan isra’ila a kasar cikin gaggawa ganin cewa jakadan baya nan domin amsa wasu tambayoyi, rahotanni sun nuna cewa yan kasar Ghana guda 7 da suka tafi Isra’ila an tsare su a filin jirgin sama, kafin daga bisani a koro guda 3 gida.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted