Shugabannin kasashen (ECOWAS) na taro a Abuja

Shugabannin kasashe mambobin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) na taro a wannan Lahadi a Abuja, fadar mulkin Najeriya. Taron, zai ba da

Shugabannin kasashe mambobin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) na taro a wannan Lahadi a Abuja, fadar mulkin Najeriya.

Taron, zai ba da damar yin bitar batutuwan da ke ci gaba dake zaman karfa kafa wa kungiyar a hanlin yanzu.

Juyin mulkin Guinea Bissau da yunkurin juyin mulkin soja a Benin, na daga cikin ajandar taron.

Shugaban kungiyar na wannan karo kana kuma shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio ya yi tir da juyin mulkin na baya bayan nan.

Batun janye sojoji kusan 200 na rundunar tsaro ta ECOWAS da aka tura Benin tun bayan yunkurin juyin mulkin a ranar 7 ga Disamba shi ma za’a tattauna a kansa.

Taron zai kuma duba halin da ake ciki a Guinea Bissau, zai kuma duba yiyuwar kakabawa kasar takunkumi bayan hambarar da Shugaba Umaro Sissoco Embalo a ranar 26 ga Nuwamba.

Kungiyoyin fararen hula da wasu kungiyoyi 17 na Yammacin Afirka suna kira ga kungiyar da ta fitar da sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa na ranar 23 ga Nuwamba ba tare da bata lokaci ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted