Kasashen AES zasu kafa bankin dogaro da kai

Kasashen yankin sahel na AES, sun kimasa game da shirin kafa bankin da zai basu damar dogaro da kai. Shugaban kasar Mali kuma shugaban kungiyar

Kasashen yankin sahel na AES, sun kimasa game da shirin kafa bankin da zai basu damar dogaro da kai.

Shugaban kasar Mali kuma shugaban kungiyar kasashen Sahel (AES), Assimi Goïta, ya karbi tawagar ministoci kudi na kasashen kungiyar don kammala kafa Bankin na zuba Jari da Ci gaba da aka tsara don rage dogaro da kudi daga waje da kuma samar da ayyukan da ke da tasiri sosai.

A lokacin wannan taron, an yi wa Shugaban kasar Mali bayani game da inda aka kwana game da shirin.

Cibiyar za ta yi aiki a bangaren kudi da nufin karfafa ikon mallakar kasashen uku.

Kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso dukkansu wadanda suka raba gari da kasashen yamma musamman faransa wacce ta yi musu mulkin mallaka na neman hanyoyin dogaro da kansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted