Isra’ila Tana Ci Gaba Da Rushe Gidaje A Yankin Gaza

   Da safiyar Yau Laraba ne sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila su ka kai hare-hare a yankuna daban-daban na zirin Gaza, tare da rushe gidaje da

 

 Da safiyar Yau Laraba ne sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila su ka kai hare-hare a yankuna daban-daban na zirin Gaza, tare da rushe gidaje da dama. Sojojin mamayar sun yi amfani da jiragen sama marasa matuki da kuma tankokin yaki domin rushe gidajen. A arewacin Gaza da gabashin Jabaliya sojojin na mamaya sun yi amfani da manyan bindigogi akan gidajen fararen hular. A unguwar “Tuffah” ma an ga yadda sojojin mamayar su ka aike da jiragen yaki marasa matuki.

A can kudancin Gaza kuwa jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ne su ka kai hare-hare akan barin Bani-Suhaila a gabashin Khan-Yunus,a lokaci daya kuma manyan bingigoginsu su ka bude wuta akan iyaka.

Tun bayan da aka tsagaita wutar yaki a cikin watan Oktoba ne, Sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ilan suke ci gaba da kai hare-hare akan Gaza ba tare da kakkautawa ba. Daga tsagaita wutar zuwa yanzu adadin Falasdinawan da su ka yi shahada a sanadiyyar hare-haren na ‘yan sahayoniya sun haura 300.

Hukumar agaji a yankin na Gaza ta yi gargadi akan cincirindon ‘yan hijira da suke rayuwa a cikin hemomin da babu kayan da rayuwa take da bukatuwa da su domin ci gaba. Ruwan sama yana ci gaba da sauka a yankuna mabanbanta na Gaza da sanyi yake karuwa ba tare da samar da na’urorin dumama hemomin ba.

Kakakin kungiyar agaji a Gaza Mahmud Basal ya ce; Suna samun dubban koke daga Gaza cewa hemomin da mutane suke rayuwa a ciki ba su dace da rayuwa ba ko kadan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted