‘Yan Isra’ila na neman a gudanar da bincike kan harin ranar 7 ga Oktoba

A Isra’ila Dubban masu zanga-zanga ne suka gudanar da wani babban gangami a Tel Aviv don neman a gudanar da bincike na gaskiya kan harin

A Isra’ila Dubban masu zanga-zanga ne suka gudanar da wani babban gangami a Tel Aviv don neman a gudanar da bincike na gaskiya kan harin ba zata na ranar 7 ga Oktoba da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta kai.

Masu zanga-zangar adawa da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu sun taru, a dandalin Habima da ke Tel Aviv, suna sake nanata bukatarsu ta kafa kwamitin bincike da aka dora wa alhakin tabbatar da gaskiya da kuma cikakken bincike kan harin na Hamas (Operation Al-Aqsa Storm).

Tsohon Firaministan Isra’ila Naftali Bennett, madugun ‘yan adawa Yair Lapid, da MK Benny Gantz, Gadi Eisenkot, da Yair Golan suma sun halarci taron.

Masu shirya taron a cikin wata sanarwa sun ce yayin da majalisar ministocin Netanyahu ke “gudun neman kafa kwamitin binciken.

A cen baya, majalisar ministocin Netanyahu ta sanar da aniyyarta ta kafa “kwamitin bincike mai zaman kansa mai cikakken iko,” tare da kwamitin ministoci da aka dora wa alhakin gabatar da umarnin kwamitin cikin kwanaki 45.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted