Iraki : Ana zaben ‘yan majalisa don tsara makomar siyasar kasar

‘Yan Iraki sun kada kuri’a don zaben sabbin ‘yan majalisar dokoki wadda za ta fayyace alkiblar siyasar kasar na tsawon shekaru hudu masu zuwa. Kimanin

‘Yan Iraki sun kada kuri’a don zaben sabbin ‘yan majalisar dokoki wadda za ta fayyace alkiblar siyasar kasar na tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Kimanin ‘yan kasar miliyan 21 ne aka tantance domin kada kuri’a ga ‘yan majalisar dokoki 329, Wadannan za su zabi shugaban kasa kuma su amince da sabuwar gwamnatin, wadda sabon firaminista zai kafa.

A cewar jami’an zabe, za a sanar da sakamakon cikin sa’o’i 24 bayan kammala zaben.

Firaminista Mohammed Shia al-Soudani ya bayyana zaben a matsayin wanda ya gudana “a cikin yanayi mai aminci da kwanciyar hankali,” yana yabon jami’an tsaro saboda kiyaye tsarin.

Al-Soudani, wanda aka zaba a shekarar 2022, yana neman wa’adi na biyu kuma zai bukaci samun rinjaye a majalisar.

A Iraki, doka ta bukaci a gudanar da zaben ‘yan majalisa akalla kwanaki 45 kafin karshen wa’adin majalisar da ke tafe.

A kasar Iraki, ana rarraba rassan gwamnati a bangarori guda uku bisa ga addini : shugabancin kasa daga bangaren Kurdawa, mukamin Firaminista daga ‘yan Shi’a sai kuma Kakakin Majalisa daga ‘yan Sunni, domin tabbatar da wakilcin dukkan bangarorin al’umma a cikin gwamnati.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted