Hamas ta sake jaddada wajabcin aiwatar da Shirin tsagaita wuta a Gaza

Wani babban kusa na Hamas ya jaddada kudirin kungiyar na tabbatar da tsagaita wuta a Gaza, yana mai jaddada cewa Falasdinawa ba sa neman komai

Wani babban kusa na Hamas ya jaddada kudirin kungiyar na tabbatar da tsagaita wuta a Gaza, yana mai jaddada cewa Falasdinawa ba sa neman komai illa ‘yancinsu na samun cin gashin kai a duniya.

Khalil Al-Haya, shugaban Hamas a Gaza, ya fadi a wata hira da aka watsa ranar Lahadi cewa bangaren Falasdinawa yana da babban kuduri tare da tabbatar da cewa ba zasu baiwa Israla wata dama ta samun hujjar dawowa da yaki a kan al’ummar Gaza ba.

Ya kara da cewa, “Al’ummar duniya, wadanda suka shahara da kuma wadanda suka yi aiki a hukumance, ba za su bari Isra’ila ta sake halasta mamayarta a kan Gaza ba.

Ya kara da cewa, Hamas ta yi matukar jajircewa kan yarjejeniyoyin da aka rattaba hannu a kansu, inda ta tabbatar da hakan ta hanyar mika fursunoni ba tare da wani bata lokaci ba.

“Mun mika fursunoni 20 daga sojojin mamaya da suke tsare sa’oi  72 bayan fara aiwatar yarjejeniyar tsagaita wuta.

Ya ce zuwa yanzu sun mika gawarwakin fursunoni 17 da suka mutu ga gwamnatin Isra’ila kuma sun kuduri aniyar nemo sauran gawawwakin.

” Za mu yi bincike da gaske kuma alhakin ne mu yin hakan, domin kare hakkokin al’ummarmu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted