An Fara Kidayar Kuri’un Zabukan Kananan Hukumomi 16 Da Aka Yi A Libya

Hukumar zaben kasar Libya ta sanar da cewa bayan da aka rufe kada kuri’u a mazabun da aka yi zaben a jiya Asabar, an fara

Hukumar zaben kasar Libya ta sanar da cewa bayan da aka rufe kada kuri’u a mazabun da aka yi zaben a jiya Asabar, an fara kidayar kuri’u.

Sanarwar ta kuma tabbaatr da cewa wadanda su ka kada kuri’un sun kai kaso 68% na jumillar wadanda su ka yi rijista,kuma an gudanar da zaben ba tare da wata matsala ba.

Fira minista Abdul Hamid Debaibah wanda yake jagorantar gwamnatin da kasashen yammacin turai su ka amince da ita a birnin Tripoli, ya yi kyakkyawan yabo akan yadda zaben ya gudana.

Ya kuma kara da cewa, zaben da aka yi ya tabbatar wa da duniya cewa al’ummar Libya za su iya tafiyar da tsarin demokradiyya.

An yi zaben ne dai na kananan hukumomi bayan da aka rika dage shi a baya saboda dalilai na tsaro.

A ranar 20 ga watan nan Okto ba ne za a yi zaben a sauran yankunan da su ka rage.

Har yanzu kasar ta Libya tana da rabuwar kawuna saboda hukumomi biyu da take da su a gabashi da kuma yammacin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted