An gudanar da zanga-zanga a sassa da dama na kasar Amurka, ciki har da manyan birane kamar New York, da Los Angeles, da Washington, da Chicago da sauransu, inda masu zanga-zangar suka rika sukar manufofin shugaba Trump na yaki da bakin haure ta hanyar amfani da karfin tuwo, da tura rundunonin jami’an tsaro zuwa wasu biranen kasar, da kara buga harajin kwastam da sauransu. Masu shirya zanga-zangar sun ce adadin mutanen da suka fito don zanga-zangar ta wannan karo ya zarce miliyoyi.
A birnin New York, mutane fiye da dubu 100 sun halarci zanga-zangar a jiya Asabar, ciki har da jagoran jam’iyyar demokrat a majalisar dattijan kasar Chuck Schumer.
Masu zanga-zangar kenan a birnin New York na adawa ne da manufofin gwamnatin Trump na korar baki da kuma girke jami’an tsaro tare da korar ma’aikata.
karo na uku ke nan da ake hada gangami tun sake hawan Trump mulki a Fadar White House a watan Janairu.
Hukumar ‘yan sandan birnin ta bayyana cewa, yawancin masu zanga-zangar sun kammala ta lami lafiya, kuma ba a kama kowa ba dangane da hakan.
Mashirya zanga-zangar sun ce miliyoyin mutane a sassan Amurka sun fita kan tituna cikin lumana, a birane da garuruwa fiye da 2700 a jiyan, kuma zanga-zangar ta wannan karo sun biyo bayan irinsu wadda aka yi a karon farko a ranar 14 ga watan Yuni da ya gabata, bisa take “No Kings” a dukkanin sassan kasar ta Amurka.