Venezuela Ta Bada Sanarwan Sabbin Matakan Tsaro A Kan Iyakar Kasar Da Colombia

Shugaban kasar Venezuelan Nicolás Maduro ya bayyana sabbin matakan tsaro a kan iyakar kasar da kasar Colombia bayan da gwamnatin Amurka ta sabonta sabbin matakai

Shugaban kasar Venezuelan Nicolás Maduro ya bayyana sabbin matakan tsaro a kan iyakar kasar da kasar Colombia bayan da gwamnatin Amurka ta sabonta sabbin matakai na nuna adawa da gwamnatin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa shugaban ya shelanta wannan sabbin matakan tsaro ne bayan da gwamnatin shugaba Trump ba bawa hukumar CIA izinin aiki tukuru don kifar da gwamnatin shugaba Madoro na kasar Venezuela.

Sabbin matakan tsaron dai sune kyautata tsaro a kan iyakar kasar da kasar Colombia wanda ya hada kan iyakoki da kasar a cikin Jihohin, Táchira, Apure, da kuma  Amazonas wadanda suke kan iyakoki mafi tsawo da kasashe makobta.

Yace tabbatar da taro a kan iyakokin kasar Colombia da wadan nan jihohi yana da matukar Muhimmanci. Yace mutanen kasar Venezuela mutanen ne wadanda suke son zaman lafiya da kuma mutunci da kuma kare mutuncinsu.

Jaridar NewYork Times ta Amurka ta nakalto shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bawa hukumar leken asiri na kasar CIA a ranar talata kan cewa ta tsara masa yadda zai kwace kasar Venezuela daga hannun Nicolas Madoro daga ciki har da kai hare-hare kan kasar idan ya kama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted