Shugaban kasar Indonusiya Prabowo Subianto ya sanar da irin ci gaban da aka samu game da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a gaza, kana ya sanar cewa Jakarta a shirye take ta aike da dakarun tabbatar da zaman lafiya, domin nuna irin tsawon lokacin da kasar ta dauka tana nuna goyon bayanta ga alummar falasdinu a gwagwarmyar neman yanci da suke yi.
Kasar Indonusiya tana da tsohon tarihi wajen nuna goyon bayan neman bada yancin ga alummar falasdinu, sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi a Gaza ya bude wata kofa ta tabbatar da zaman lafiya a yankin, kuma kasar a shirye take ta aike da kayan agaji, bangaren diplomasiya, aikewa da dakarun tabbatar da zaman lafiya domin ganin an samu zaman lafiya mai dorewa.
Shugaban kasar na Indonusiya ya bayyana zaman lafiyar da aka samu a baya bayan nan a gaza, a matsayin wani mataki na samun tabbaci, kuma yayi ishara game da kalubalen da ake fuskanta, inda yace indunusiya ta yarda da zaman lafiya, taimakon agaji a yanki, kana kuma ya jaddada shirin kasar na bada duk wata gudunmawa wajen aikewa da dakarun tabbatar da zaman lafiya na kasa da kasa.