Isra’ila  Za Ta Sake Kai Hare-hare Idan Ta Karbi Dukkan Mutanenta Da Hamas Ta Kama.

Ministan kula da ayyukan soji na HKI Katz ya bayyana cewa dakarun sojin Isra’ila za su koma da kai hare-hare a yankin Gaza, bayan ta

Ministan kula da ayyukan soji na HKI Katz ya bayyana cewa dakarun sojin Isra’ila za su koma da kai hare-hare a yankin Gaza, bayan ta kammala karbar dukkan mutanen ta da kungiyar Hamas ta kama, don nuna rashin amincewa da sabuwar yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma tsakanin Hamas da kuma gwamnatin tel Aviv.

Isra’ila tana fuskantar babban kalubale wanda bayan dawo da dukkan mutanen ta da aka kama, shi ne batun lalata dukkan ramukan hamas dake yankin Gaza kai tsaye ta hanyar sojoji kuma ta hanyar tsarin kasa da kasa da za’a kafa karkashin umarnin da kulawar Amurka,

Wannan yana zuwa ne kwana daya kafin kulla yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakanin hamas da Isra’ila, da shiga tsakanin kasashen Qatar Masar da kuma kasar Amurka domin kawo karshen dogon yakin daka kwashen shekaru biyu ana yi a Gaza.

Ko a jiya ma sojojin isra’ila sun kashe falasdinawa guda 9 a daidai lokacin da sojojin ke gargadin falasdinawa da su guji  zama a yan kunan da har yanzu suna cikin mamaya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted