Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Jirgin Ruwa Da Ke Hulda Da Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Sojojin Yemen sun kai hari kan wani jirgin ruwa da yake hulda da haramtacciyar kasar Isra’ila da makami mai linzami Dakarun sojin Yemen sun sanar

Sojojin Yemen sun kai hari kan wani jirgin ruwa da yake hulda da haramtacciyar kasar Isra’ila da makami mai linzami

Dakarun sojin Yemen sun sanar da cewa, da sanyin safiyar ranar Larabar nan, sun kai hari kan jirgin (MINERVAGRACHT) da makami mai linzami a mashigin tekun Aden.

Sanarwar da Rundunar Sojin Yemen ta fitar ta tabbatar da cewa: Sojojin ruwan kasar sun kai wani samame na soji kan jirgin Ruwan na (MINERVAGRACHT) saboda kamfanin ya keta dokar hana shiga tashar jiragen ruwa na Falasdinu da aka mamaye. Sanarwar ta bayyana cewa an kai harin ne a mashigin tekun Aden tare da wani makami mai linzami, wanda ya yi sanadin harbo jirgin kai tsaye tare da kama jirgin. Yanzu yana cikin hadarin nutsewa.

Rundunar sojin kasar ta Yemen ta bayyana cewa: Wannan farmakin ya zo ne a cikin tsarin kare al’ummar Falastinu da ake zalunta da kuma ‘yan gwagwarmayarsu masoya, tare da mayar da martani kan laifukan kisan kiyashi da yunwa da makiya yahudawan sahayoniyya suka aikata a kan ‘yan’uwansu a zirin Gaza, tare da tabbatar da ci gaba da haramta zirga-zirgar jiragen ruwa ga makiya ‘yan sahayoniyya a tekun Red Sea da Larabawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted