A yau Najeriya ke bikin cika shekaru 65 da samun yancin kai

Yau Najeriya ke cika shekaru 65 da samun ƴancin kai daga Turawan mulkin mallaka, inda aka saba gudanar da bukukuwa da kuma nazari dangane da

Yau Najeriya ke cika shekaru 65 da samun ƴancin kai daga Turawan mulkin mallaka, inda aka saba gudanar da bukukuwa da kuma nazari dangane da ci gaban da ƙasar ta samu a ƙarƙashin mulkin ƴan ƙasa da kuma ƙalubalen da take fuskanta.

Bikin na bana na zuwa ne a daidai lokacin da jama’ar ƙasar ke rayuwa a cikin mawuyacin hali, sakamakon taɓarɓarewar tattalin arziki da tsadar rayuwa waɗanda suka biyo bayan sauye-sauyen da gwamnatocin da suka gabata da kuma mai ci suka ƙaddamar da zummar sake fasalin tafiyar da ƙasar.

A irin wannan rana a shekarar 1960, aka rantsar da Dr. Nnamdi Azikiwe a matsayin shugaban ƙasa, tare da Sir Abubakar Tafawa Balewa a matsayin Firaminista, shugabannin da suka yanke wa ƙasar cibiya da kuma shimfiɗa mata hanyoyin ci gaba a bangarori da dama, kafin juyin mulkin da sojoji suka musu a ƙarƙashin jagorancin Janar Johnson Aguiyi Ironsi, wanda ya yi sanadiyar kashe Firaministan da Firimiyar Arewa, Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto da kuma wasu fitattun ƴan siyasa.

A wadɗannan shekaru 65 Najeriya ta fuskanci matsaloli da dama tare da samun ci gaba a wasu fannoni da kuma koma baya a wasu bangarorin.

Daga cikin irin ci gaban da ƙasar ta samu akwai yawan jama’a masu kuzari da kuma ƙoƙarin ganin an samu ci gaba a ɓangarori daban-daban da suka haɗa da noma da kiwo da kasuwanci da ma’adinan ƙarƙashin ƙasa waɗanda suka taka gagarumar gudumawa wajen sanya ƙasar a sahun gaba wajen ci gaba a nahiyar Afirka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted