Majalisar Dinkin Duniya Ta Sake Kakabawa Iran Takunkumin Rashin Adalci

Majalisar Dinkin Duniya ta sake sanyawa Iran takunkumin rashin adalci a hukumance A hukumance Majalisar Dinkin Duniya ta sake kakabawa Iran takunkumi mai tsauri kan

Majalisar Dinkin Duniya ta sake sanyawa Iran takunkumin rashin adalci a hukumance

A hukumance Majalisar Dinkin Duniya ta sake kakabawa Iran takunkumi mai tsauri kan shirinta na makamashin nukiliya da take gudanarwa ta hanyar lumana, ta hanyar amfani da tsarin da aka fi sani da “Snapback”.

Matakin na Majalisar Dinkin Duniya ya samo asali ne daga zargin karya da ake yi wa Iran na karya yarjejeniyar makamashin nukiliyar da aka kulla a shekarar 2015 da Amurka, da Birtaniya, da Rasha, da Faransa, da China da kuma Jamus. Wannan shawarar dai ta zo ne duk da irin jajircewar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kan yarjejeniyar, da ficewar Amurka daga cikinta a shekara ta 2018, da kuma kasashen Turai uku, wato Birtaniya, Faransa da Jamus, da suka yi watsi da wajibcin da suka rataya a wuyansu.

Iran za ta sake fuskantar takunkumin hana shigo da makami, da haramta duk wasu ayyukan inganta sinadarin Uranium, da kuma duk wani aiki da ya shafi makami mai linzami da ke iya daukar kawunan makaman nukiliya, ciki har da harba su.

Sauran takunkuman da za a sake sanyawa sun hada da haramtawa Iraniyawa da dama tafiye-tafiye, da hana kadarori da dama na daidaikun mutane da hukumomin Iran, da kuma hana samar da duk wani abu da za a iya amfani da shi a shirin makamashin nukiliyar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted