Shugaban Majalisar Tsaron Kasar Iran  Dr Ali Larijani  Ya Isa Birnin Berut .

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban majalisar tsaro na kasar iran Dr Ali larijani ya isa birnin berut na kasar labanon, kuma ya gana da shugaban

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban majalisar tsaro na kasar iran Dr Ali larijani ya isa birnin berut na kasar labanon, kuma ya gana da shugaban majalisar dokokin kasar Nabi birri  ya kuma bayyana ta a matsayin mai amfani sosai domin ta mayar da hankali kan yadda zaa kara kyautata alaka tsakani.

Haka zalika larijani ya nuna fatansa na ganin an hada kai domin samar da wani karfi guda daya da zai iya tunkarar makircin da Iisra’ila ke kitsawa.

Kana ya jinjinawa shirin da sakatare janar din kungiyar hizbullah ya bullo da shi na  tattaunawa da kasar Saudiya, kuma ya bayyana hakan  a matsayin babbar dabara.

Haka zalika ya jaddada matsayin hizbullah a matsayin wani babban shamaki ga Isra’ila, kuma masu karfin sadaukarwa a cikin alumma, kana ya bayyana tsayin daka a  matsayin wata babbar kadara ga duniyar musulmi.,

.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted