Tashar talabijin din “NBC” ta Amurka ta bayar da labarin cewa gwamnatin Amurka tana Shirin kai harin soja akan wasu wurare a cikin kasar Venezuela.
Tashar talabijin din na NBC ta ambato wasu majiyoyi 4 na Amurka da su ka bayyana cewa shugaban kasar Donald Trump bai kai ga bayar da umarnin kai harin ba, amma kasar ta Amurka tana tattaunawa da Venezuela ta hanyar wata kasar gabas ta tsakiya.
A cikin makwannin bayan nan dai Amurkan ta kai wasu hare-hare akan kananan jiragen ruwan da suke fitowa daga kasar ta Venezuela tana mai zargin cewa suna dauke da muggan kwayoyi.
A ranar 2 ga watan Disamba din nan ne dai shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya sanar da cewa kasarsa ta kai hari akan wani jirgin ruwa da ya fito daga kasar Venezuela.