Iran Ta Nuna Bayanan Sirri Na Cibiyoyin Nukiliyar HKI

Hukumar Leken Asiri ta Iran ta fitar da wasu bayanai na sirri da suke da alaka da ayyukan cibiyar makaman Nukiliyar HKI. Bayanan da ma’aikatar

Hukumar Leken Asiri ta Iran ta fitar da wasu bayanai na sirri da suke da alaka da ayyukan cibiyar makaman Nukiliyar HKI.

Bayanan da ma’aikatar leken asirin ta Iran ta fitar wadanda aka watsa a kafafen watsa labarun kasar, sun kuma kunshi ayyukan da wasu masana a fagen Nukiliya na turai suke gudanarwa.

 Majiyar tsaron ta Iran ta kuma ce bayanan da ta samu suna kunshe a cikin miliyoyin shafukan takardu, sun kuma same su ne ta hanyar wasu cibiyoyi na ‘yan sahayoniya da kuma cibiyarta ta Nukiliya.”

 Ministan hukumar leken asirin ta Iran ya ce, an shigo da miliyoyin takardun masu kunshe da wadannan bayanan zuwa cikin Iran, suna kuma kunshe da bayanai masu kima.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted