Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Yamen sun kaddamar da wani hari da jiragin sama mara matuki a filin jirgin sama na Isra’ila domin nuna goyon bayansu ga alummar palasdinu adaidai lokacin da isra’ila ke ci gaba da yin kisan gilla a gaza.
Kakakin sojojin kasar yamen brigadier ganar Yahaya Saree ya sanar a gidan talabijin cewa yau ma dakarun sojin kasar sun kai wani hari da jirgin sama mara matuki da ya keta sararin samaniyar isra’ila ya dira a filin saukar jiragen sama na Ramon,
Tuni dai dakarun kasar yamen suka sanar da aniyarsu ta ci gaba da kai hare hare kan isra’ila har sai ta dakatar da kai hari da yin kisan kiyashi kan alummar gaza. Ya zuwa yanzu isra’ila ta kashe palasdinawa sama da 64,800 mafi yawanci kuma mata ne da yara kanana.