Isra’ila Za ta Gamu Da Mummunar Martani Idan Tayi Gigin Afkawa Iran

Ramezan sharif  wani babban jami’I yace idan gwamnatin HKI ta yi kuskure kan kasar Iran, za ta fuskanci mayar da martani mai tsananin, yace ba

Ramezan sharif  wani babban jami’I yace idan gwamnatin HKI ta yi kuskure kan kasar Iran, za ta fuskanci mayar da martani mai tsananin, yace ba zamu jira taimakon kowa ba wajen kare kasarmu domin muna da karfi wajen kare kasa.

Da yake Magana a gaban manema labarai a wajen bikin cika shekaru 2 na ambaliyar alaqsa wanda dakarun gwagwarmayar yanto palasdinu suka kaddamar kan HKI,yace harin ya fantsama alamarin falasdinu a duniya,

Har ila yau ya kara da cewa harin na 7 ga watan oktoban shekara ta 2023 ya nuna cewa isra’ila ba ta da wahalar yin galaba akanta, kuma al’ummar Palastinawa sun kuduri aniyar ci gaba da gwagwarmaya da gwamnatin mamaya da ta shafe shekaru tana aiwatar da kisan gilla kan al’ummar kasar.

Sharif ya ci gaba da yabawa Operation al-Aqsa a matsayin “babban nasara ga al’ummar Palastinu,” yana mai cewa hakan ya haifar da goyan bayan duniya ga Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted