An Zabi Issa Tchiroma A Matsayin Dan Takara Daya Tilo A Kamaru

Bayan kwashe makonni manyan ‘yan takara a jam’iyyun adawa da sauran jiga-jigan ‘yan siyasa na tuntubar juna domin ganin an fitar da dan takara daya

Bayan kwashe makonni manyan ‘yan takara a jam’iyyun adawa da sauran jiga-jigan ‘yan siyasa na tuntubar juna domin ganin an fitar da dan takara daya tilo, da yammacin ranar Asabar 13 ga watan nan na Satumba, 6 daga ciki sun amince da tsohon minista kuma mafi kusanci ga gwamnati tsawon shekaru 16,

wanda ya taba zama mai magana da yawun gwamnati a matsayin wanda zai fafata da Paul Biya na jam’iyyar RDPC wanda ya kwashe sama da shekaru 42 ya na mulkin kasar da ke tsakiyar Afirka.

An zabe shi ne daga cikin ‘yan takara na jam’iyyun adawa 6 cikin 12 da hukumar zabe ta tabbatar da su a matsayin wadanda suka cancanci takara, karkashin inuwar gamayyar Union du Changement.

To sai dai hakan baya nufin cewa sauran ‘yan takara sun je kenan a cewar gamayyar , za’a ci gaba da yin haÉ—in gwiwa domin janyo sauran ‘yan takara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted