Mataimakiyar shugaban kasar Venezuela Delcy Rodriguez ta yi gargadi game da shirin Washington na kara ruruta wutar rikicin soji a yankin Latin Amurka, tana mai zargin Amurka da neman sauyi gwamnati a Venezuela da kuma sarrafa albarkatun kasar.
Rodriguez ta bayyana cewa “kasancewar sojojin Amurka a yankin Caribbean na nufin aiwatar da sauyin gwamnati a Venezuela da kuma mamaye dukiyarta.” Ta kara da cewa, biyo bayan gazawar takunkumi da tsare-tsare na tattalin arziki, Washington ta “yanke shawarar haddasa yaki a wannan bangare na duniya,” tana mai jaddada cewa duk wani harin soji a kan Venezuela “zai haifar da rashin kwanciyar hankali a yankin Latin Amurka.”
Mataimakiyar shugaban kasar ta Venezuela ta yi watsi da zargin da Amurka ta yi a kan Shugaba Nicolas Maduro na fataucin miyagun kwayoyi a matsayin “babbar farfaganda” da kuma neman bata sunan halastacciyar gwamnatin Venezuela.”
Kalaman Rodriguez sun zone daidai da sanarwar da shugaba Maduro ya bayar na tura dakaru 25,000 a gabar tekun Caribbean da kuma kan iyakar kasar da Colombia, a daidai lokacin da ake samun takun saka tsakaninsa da shugaban Amurka Donald Trump.