Shugaban Najeriya Ya Bada Da Umarnin Karya Farashin Kayan Abinci

Rahotanni sun bayyana cea Shugaban nigeria Bola Tinubu ya umarci wani kwamiti na Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da ya dauki matakai don karya farashin

Rahotanni sun bayyana cea Shugaban nigeria Bola Tinubu ya umarci wani kwamiti na Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da ya dauki matakai don karya farashin abinci a fadin Najeriya.

Sanata Sabi Abdullahi, Ministan Noma ne, ya bayyana hakan a lokacin wani taron horaswa na kwana daya ga ‘yan jarida a Abuja ranar Laraba. Ya ce shirin rage farashin kayan abinci ya hada da tabbatar da cewa kayan noma suna tafiya cikin tsari da farashi mai sauki.

Sanata Abdullahi ya kara da cewa, tsadar jigilar kayan amfanin gona shi ne daya daga cikin dalilan da ke sanya abinci ya yi tsada a kasuwanni. Ya ce kwamitin na FEC yana aiki don tabbatar da jigilar kayan amfanin gona sun zama masu sauki, wanda zai taimaka wajen rage farashin abinci.

Ya ce wannan mataki yana cikin hangen nesan Shugaba Tinubu a kan abinci, wanda ke nufin samar da abinci mai sauki ga kowa. .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted