Isra’ila Ta Kai Hari Kan Jagororin Hamas A Doha

Jiragen yakin HKI sun kai hare-hare kan cibiyar gudanarwa na kungiyar Hamas dake birnin Doha na kasar Qatar dazo da rana. Tashar talabijan ta Presstv

Jiragen yakin HKI sun kai hare-hare kan cibiyar gudanarwa na kungiyar Hamas dake birnin Doha na kasar Qatar dazo da rana.

Tashar talabijan ta Presstv a Tehran ta nakalto tashar talabijan ta 13 ta Haramtacciyar Kasar Isra’ila na bada labarin cewa jiragen yahudawan sun kai hare-haren ne a dai-dai lokacinda shuwagabannin kungiyar Hamas suke taro don tattauna sabon shawarar da shugaban kasar Amurka Donald Trump ga bagatar don tsagaita wuta tsakanin HKI da kungiyar a Gaza.

Labarin ya kara da cewa shugaban kungiyar Khalil Al-Hayya, da Zaher Jabiran shugaban reshen kungiyar yankin yamma da kogin Jordan, da kuma Khalid Mash’al duk suna cikin taron. HKI ta kira hare-haren, da sunan hare-haren kissan shuwagabannin Hamas.

Amma gwamnatin kasar Qatar ta yi allawadai da hare-haren ta kuma bayyana su na ‘Matsorata’ . sannan ta kara da cewa dukkan shuwagabannin kungiyar sun tsira daga hare-hare. Majiyar kungiyar ta fadawa tashar talabijin ta Al-Jajira kan cewa, Al-Hayya shugaban kungiyar ya tsira, haka sauran shuwagabannin gungiyar.  Sannan wannan wasu kafafen yada labaran sun bayyana cewa HKI ta kai wadan-dan hare-hare ne tare da amincewar shugaban kasar Amurka Donald Trump. A dai dai lokacinda ya san cewa wadanan shuwagabannin Hamas zasu taru don tattauna abinda ya kira shawararsa ta karshe na dakatar da yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted