Iran za ta wanzar da hadin kai a duniyar Musulmi (Pezeshkian)

Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa Iran ba ta neman fada da wata kasa ta musulmi ba, kuma tana ci gaba da

Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa Iran ba ta neman fada da wata kasa ta musulmi ba, kuma tana ci gaba da jajircewa wajen ingantawa da kuma wanzar da hadin kai a tsakanin kasashen musulmi.

Da yake jawabi a taron kasa da kasa na hadin kan musulmi karo na 39 a birnin Tehran, Mr. Pezeshkian ya bayyana cewa babu wani mahaluki da zai iya cin galaba a kan musulmi idan har suka ci gaba da kasancewa tare da tabbatar da adalci a cikin al’ummominsu.

Ya kara da cewa, idan musulmi kan su ya hade waje guda, ba tare da wani rikici ba, sahyoniyawan ba za su taba aikata irin wadannan laifuka a Gaza da kasashen yankin ba.

Daga nan sai ya bayyana fatansa cewa tarurrukan da ake yi tsakanin al’ummar musulmi za su haifar da hadin kai, yana mai cewa taron na Tehran na da nufin “rusa katangar rarrabuwar kawuna da samar da hadin kai” a tsakanin musulmi.

A wani bangare na jawabin nasa, Mr. Pezeshkian ya tunatar da cewa, Amurka da gwamnatin Isra’ila sun kasa cimma munanan manufofinsu a yakin kwanaki 12 da Iran, “saboda hadin kanmu.”

Shugaba Pezeshkian ya kuma mika godiyarsa ga kasashen musulmi kan yadda sukayi Allah wadai da laifukan da gwamnatin Isra’ila ta aikata, kafin ya jaddada muhimmancin karfafa hadin kai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted