An Kaddamar da kungiyar tallafawa kasuwanci tsakanin kasashen Afirka

A wani mataki na tallafawa kasuwanci tsakanin kasashen Afrika an kaddamar da wat kungiyar mai manufartallafawa kasuwanci tsakanin kasashen Afirka tare da saukaka ayyukan raya

A wani mataki na tallafawa kasuwanci tsakanin kasashen Afrika an kaddamar da wat kungiyar mai manufartallafawa kasuwanci tsakanin kasashen Afirka tare da saukaka ayyukan raya kasa da sarrafa albarkatun cikin gida.

Bankin shigo da kayayyaki na Afirka ne ya kaddamar da kungiyar Don tallafawa kasuwanci, fitar da kayayyaki, da sarrafa albarkatun kasa a Afirka, wanda aka sanar da kirkiro da shi a yayin bikin ranar Afirka.

Shugaban bankin Afrexim Bank Oramah Benedict ne ya sanar da hakan a hukumance a birnin Algiers, a yayin bikin ranar ‘yan kasashen Afirka.

An gudanar da bikin ne a gefen ranar al’ummar kasashen Afirka, wanda firaministan rikon kwarya na kasar Aljeriya Sifi Ghrib ya jagoranta, tare da halartar jami’ai daga Afirka da dama.

Ayman El-Zoghby, daraktan sashen kasuwanci da hada-hadar kudi, kasuwanci da zuba jari na bankin Afreximbank, ya bayyanawa kanfanin dillancin labaran kasar Aljeriya (APS) cewa wannan sabuwar cibiyar tattalin arziki na da burin samar da karin kima ga kayayakin da ake sarafawa a kasashen nahiyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted