Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa 50 A Harin  Da Takai A Yankin Gaza

Kasashen Duniya da dama ne suka damu game da irin halin da ake ciki a yanki gaza da kuma yadda yake kara ta’azzar inda adadin

Kasashen Duniya da dama ne suka damu game da irin halin da ake ciki a yanki gaza da kuma yadda yake kara ta’azzar inda adadin wadanda ke mutuwa yake kara yawa sosai kullum fiye da kowanne lokaci.

Yanayin tsarin ilimi a Gaza yana gab da rushewa baki daya, inda makarantu da dama ko dai an rusa su,ko kuma sun koma sansanin yan gudun hijira, sojojin Isra’ila da gangan suke kai hari Asibitoci da wuraren kula da lafiya,  jami’an bada agaji sun yi  gargadin cewa idan yanayin ya ci gaba da tafiya a haka zai zama babban balai musamman ga yara kanana,a bangaren kwakwalwa da kuma ci gaba.

Sai dai isra’ila ta yi ikirarin cewa dukkan hare-harenta tana kai wa a wuraren soji ne, sai dai kungiyoyin kare hakkin bil adama da kungiyoyin majalisar dinkin duniya sun sanar cewa adadin fararen hula da ake kashewa sun yi yawa sosai yayin da abubuwan da suka shafi ilimi kuma an lalata su baki daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted