Manyan Jami’an Kungiyar Hamas sun Gana Da Minister Harkokin Wajen Iran

Khalil al -Hayya shugaban kungiyar Hamas a yankin gaza dake falasdinu tare da yawa daga cikin mambobin kungiyar Hamas da jagororinta na siyasa sun gana

Khalil al -Hayya shugaban kungiyar Hamas a yankin gaza dake falasdinu tare da yawa daga cikin mambobin kungiyar Hamas da jagororinta na siyasa sun gana da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi a birnin Doha na kasar Qatar, inda suka tattauna game da yakin kwanaki 12, da hakan ke nuna irin goyon baya da iran take bawa yan gwagwarmayar falasdinu ,wanda ya sanya wasu kasashen turai suka amince da falasdinu a matsayin kasa

Amurka da HKI suna shirin ganin sun kwashe mutanen Gaza sai dai Arqchi ya aike da sako mai karfi zuwa ga Amurka da HKI a taron da suka yi da jami’an kungiyar hamas a gaza, na irin shirin da iran take da shi na ci gaba da goyon bayan yan gwagwarmaya  yadda zasu ci gaba da wanzuwa a yanki

Ana sa bangaren shugaban kungiyar hamas Al-Hayya ya gabatar da rahoto game da halin da ake ciki a yankin gaza, inda yayi kira ga kasashen duniya da su taimaka wajen ganin an kawo karshen killace gaza da ka yi da kuma aikewa da kayayyakin agaji tare da fuskantar siyasar Isra’ila, wadanda ke ci gaba da mamaya da kuma yin kisan kiyashi da haifar da rikice-rikice a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted