Asusun “UNICEF” Ta Jaddada Takaicinta Kan Hana Yaran Falasdinawa Samun Ilimi

Asusun kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya “UNICEF” ta bayyana cewa: An tauye hakkokin yaran Gaza na ‘yancin samun ilimi, kuma makarantu sun

Asusun kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya “UNICEF” ta bayyana cewa: An tauye hakkokin yaran Gaza na ‘yancin samun ilimi, kuma makarantu sun zama matsugunan ‘yan gudun hijira

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana a jiya Juma’a cewa: An tauye hakkokin yara a zirin Gaza tun daga hakkin samun ’yancin ilimi, inda a yanzu haka makarantu sun zame matsugunan ‘yan gudun hijira, saboda an rusa musu gidaje ko lalata musu, yara ba su da wurin koyon ilimi. Kungiyar ta kara da cewa “fiye da yara 700,000 a Gaza ba su da ilimin boko.”

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta fada a jiya Juma’a cewa sanarwar da Katz ya yi na kara kai hare-hare a Gaza kalubale ne ga dokokin kasa da kasa da kuma amincewa da jama’a sun aiwatar da kisan kiyashi da kuma tilastawa Falasdinawa gudun hijira.

Kungiyar ta yi kira ga Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kuma bangaren shari’a na kasa da kasa da su gaggauta daukar matakin shawo kan masu aikata laifukan yaki, da jagororin ‘yan mamaya, da kuma dora musu muggan laifukan cin zarafin bil’adama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted