Iran ta yi Allawadai da kisan jami’an gwamnatin Yemen da Isra’ila ta yi

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan kisan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi wa  wasu daga cikin manyan jami’an

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan kisan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi wa  wasu daga cikin manyan jami’an kasar Yemen, tare da yin kira ga al’ummar duniya da su tinkari irin wadannan munanan ayyuka  na rashin bin doka da oda.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar ta yi tir da wadannan ayyuka na  ta’addanci, tare da jaddada bukatar  daukar matakin gaggawa daga kasashen duniya don dakile aniyar yahudawan sahyuniya ta kawo hargiti a gabas ta tsakiya, wanda kai tsaye yake shafar tsaro na kasashen duniya.

Ta bayyana wannan munanan aiki da cewa, ba wai kawai laifukan yaki da laifin cin zarafin bil’adama ba ne, har ma  yana a matsayin ramuwar gayya da nufin dakile kudurin al’ummar Yemen na tallafawa al’ummar Palastinu da ake zalunta.

Sanarwar ta zo ne bayan hare-haren da Isra’ila ta kai kan babban birnin kasar Yaman Sanaa, wanda ya yi sanadiyar mutuwar firaministan kasar Ahmed Ghaleb Al-Rahawi, a lokacin da suke gudanar da taro na gwamnati tare da wasu jami’a da ministoci.

Hare-haren sun zo ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke bayar da gudunmawarta wajen tallafawa a al’ummar Gaza, da nufin ganin gwamnatin yahudawan sahyuniya ta kawo karshen kisan kiyashin da take yi dare da rana a kan mata da kananan yara a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted