Francesca Albanese, Jami’a mai tattara bayanai kan al-amuran Falasdinawa a MDD ta yi tir da gwamnatin kasar Jamus dangane da yadda jami’an tsaron kasar suke dirar mikiya kan masu goyon bayan Falasdinawa a birnin Berline.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Albanese tana fadar haka a yau Jumm’a ta kumamkara da cewa: Ina kiran mutanen Jamus kan cewa ku ne kuka samar da ikidar Nazi, a yayinda mu a kasar Italia da Spaine muka samar da akidar Fasim a nahiyar turai a baya, wana ya kai kasashen turai ga lalacewa..
Jami’ar ta bayyana haka ne bayan dirar mikiyan da jami’an tsaro na Jamus suka yi kan masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa wadanda kuma suke bukatar HKI ta kawo karshen kisan kiyashin da ke faruwa a gaza, da kuma kissan wani dan jaridan da sojojin HKI suka yi a cikin yan kwanakin da suka gabata.
Hotunan bidiyon da aka yada ya nuna yadda yansandan kasar Jamus a birnin Berline suke dokan wani mai zanga-zangar Lumana, a kan fuskansa har sai da suka zubar da jini daga hancinsa.
HKI dai ta kashe Falasdinawa fiye da dubu 63 a gaza tun cikin watan Octoban shekara ta 2023. Wannan ya sa masu goyon bayan Falasdinawa a duk fadin duniya suke fita kan tituna don neman a kawo karshen wannan yakin. Daga ciki hatta kotun ICC ta fadda sammacin kama Natanyahu shugaban gwamnatin HKI. Da kuma tsohon ministan yakinsa Yauf Galant.