Aragchi: Iran Zata Maida Martani Ga Kasashen Turai Dangane Da “SnapBack”

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a zantawa ta wayar tarho da ministocin harkokin wajen kasashen Turai guda uku wato E3, ya ja kunnensu

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a zantawa ta wayar tarho da ministocin harkokin wajen kasashen Turai guda uku wato E3, ya ja kunnensu kan sake maida takunkuman MDD da ke cikin yarjeniyar JCPOA. Ya gargadesu kan cewa Tehran zata maida martanin da ya dace da aikinsu.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa daukar wannan matakin zai kawo karshen yarjeniyar JCPOA ta shekara 2015. Sannan Iran zata sauya dukkan al-amuranta da suka shafi makamashin nukliya. Banda hakan wannan zai raba kan manya-manyan kasashen duniya dangane da shirin makamashin nukliya na kasar Iran.

Snapback dai wani shiri ne da ke cikin yarjeniyar JCPOA wacce manya-manyan kasashen duniya 5+1, wato kasashen mambobi na din din din a kwamitin tsaro na MDD tare da kasar Jamus suka amince da shi a cikin yarjejeniyar kan cewa idan sun ga Iran taki aiwatar da wani abu a cikin yarjeniyar zasu sake maida takunkuman MDD a kanta.

Amma abinda ya faru bayan yarjeniyar shi ne Iran kadai ta yi amfani da dukkan alkawulan da ta dauka a yarjenita amma kasashen kasashen turai da Amurka sun sun fice –kamar Amurka- ko kuma sun ki aiki da ita. Sannan a yanzun kasar Iran ta ta rike alkawalinta har zuwa yanzu zasu yi

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted