Tawagar Sudan karkashin jagorancin babban daraktan hukumar leken asiri ta kasa (NISS) Manjo Janar Ahmed Mufadal ta isa Mogadishu babban birnin kasar Somalia a wata ziyarar aiki da ta kai kasar, inda ta gana da shugaban kasar Hassan Sheikh Mohamud a fadar shugaban kasa dake Mogadishu.
Jagoran tawagar ta Sudan Mufadal Sheikh Mohamud ya aike da sako daga shugaban kwamitin rikon kwarya na kasar Sudan, Laftanar Janar Abdel Fattah Al-Burhan.
Sakon ya hada da jaddada aniyar Khartoum na karfafa hadin gwiwa da Somaliya, musamman a fannin tsaro da leken asiri.
Taron ya samu halartar babban daraktan hukumar leken asiri ta kasar Somalia Mahad Mohamed Salad, wanda ya tattauna da Mufadal hanyoyin inganta hadin gwiwa domin tunkarar kalubalen da yankin nasu ke fuskanta.